Harshe
Harshe
Harshe
Jirgin Malam Buɗe Ido
Ku kasance cikin shirin kafa almajirai na Kristi daga cikin mutanen dake bukatar bishara a Duniya. Kamar Filfilo dake tashi cikin hanzari a tazara mai nisa, yana barbarar kowacce fulawa da ya samu, muna addu’a masu bi suyi koyi da wannan wajen shelar Bishara a duk inda suka tafi.
Mun gaskata cewa Makarantar Live School tafi kyau wajen kafa Ikkilisiyai wanda zasu tabbata. Yin amfani da wannan hanya ta ratsa al’adu nada karfi sosai, a maida hankali ga almajirci na tsawon wata 6-18, muna so muga an samun a kalla Mishinari Miliyan daya a fadin duniya nan da 2030. Mun bada gaskiya Allah zai kawo gagarimin canji, domin wannan shine lokacin. Girbin da yawa kuma a kwai bukata ta gaggawa ga mu Krista mu sa kai.
Idan wannan hange ya taba zuciarku, ku hada hannu da mu. Ku kasance cikin tafiyar.
Ka kara karntawa nan kasa ko nemi yin rigista anan sama
“Abin ban shaa’wa ne ganin yadda a karshe wannan kayan aikin sun kai ga hannun mutane. Ina ganin wannan zai yadu a dukan Amerika ta Tsakkiya”.
“Bidiyo akan manhaja, wanda aka shirya musamman domin kafa ikkilisiyai, rubanbanyawa da koyar da shugabanci, yayi dai dai da rayuwar karkara a inda Ikkilisiyai ke yaduwa”.
“kasha 70% na dalibanmu sun shiga karkara don kafa Ikkilisiya”.
“babban aiki domin Ikkilisiyai shine yadda za’a gargadi mutane ga aikin bishara. Makarantar Live School itace amsa ga wannan matsala”.
Bettie
Mission to Guatemala
Alok
Pastor a Indiya
Felix
Pastor a Zambia
Duman
Pastor a Kazakhatan
Akwai abubuwa da yawa da za’a kula dasu wanda zaka bukaci daukar shawara kafin ka fara Makarantar Live School. Suna kamar haka:
Kafin ka kalli Bidiyo
1) Makarantar ana iya yinta na “cikakken lokaci” ko “rabin lokaci”.
-
- A Makrantar cikakken lokaci zaku bukaci ku shiga aji sau uku kowacce rana, zai dauke ka watanni 18 a gama.
- A makarantar rabin lokaci zaku bukaci yin watanni 18. Sai ku shirya yadda zaku raba manhajar bisa ga lokacin da zaku dauka.
- Hanya mai kyau ta gudanar da Makarantar shine, a hada iyali da abokai su hada akai don koyi. Ta wannan hanyar zaku taimaka wajen koyar da mutane dayawa don shelar Bishara ga batattu. Duk da haka, yana kyau idan zaka bi Manhajr don kashin kanka, musamman idan kana zaune a wurin dake da hadari ko kasar dake da matsala.
- Idan kuna kungiya, zamu so kusa wannen su yayi rigista a sashen yanar gizo don mu san irin cigaban da suke samu.
- Yafi kyau a ajiye lokaci domin Makarantar Live School domin kowa ya kasance da jaddawalin a hannusa.
- Wata hanyar kuma itace, kusa ‘yan kungiyarku su kalli sassan bidiyon a kadaice ko kungiyance na kashin kansu, su kuma tantauna tsakaninsu.
Yayin da kuke kallon
2) Sadda kuka zo tare, sai kuyi addu’a daga nan a nuna bidiyon, (yanada mahimmanci a fara duba yadda tsarin dukan bidiyon yake sashe sashe, daya bayan daya yadda aka shirya shi, saboda Makarantar an shiryata ta hanyar dake gina dadliban daga wannan mataki zuwa wannce).
-
- Lokacin da ake duba bidiyo sai ka rubuta abubuwan da sukayi maka fice.
- Da zarar an kamala sashen, ku dauki lokaci ku tantauna abinda kowa ya koya daga ciki. Ka kafafa kowa ya rubuta abinda ya tsallake a cikin rubuntunsa.
- Da zarar kun je gida, kuyi amfani da abinda kuka dauko a rubuce ku rubata shafi daya na abinda kuka koya, zaifi kyau a shirya shi kamar za’ayi wa’azi. (a shirya shi kwaya kwaya).
- Daga an a hau da wannan shafi gudan akan yanar gizo ta sashen mu. Zaku iya daukar hoto ku aika ba sai anyi amfai da ‘sikana’ ba.
- Ku boye wannan shafi daya a fayal doming aba.
- Ka ci gaba da bin wann hanya har a gama kos din.
Da zarar ka gama da sassan Makarantar Live School
3) Za’a baka satifiket na kamala Makarantar Live School muddin ka cika wadan nan sharudd guda uku.
-
- Ka bi ciki manhajar (awa 242).
- Ka aika da shafi dai dai din nan 242 a yana gizo.
- Ka nemi a baka satifiket dinka ta hannar Yanar-gizo kuma ka dangwala “Application for Certificate completion.”
4) Idan kana so ka kara karatu a South African Theological Seminary (SATS) ko Theolgical Institute of Argentina (FIFT), zaka iya ka nemi a baka shaidar takarda sassan da kayi ta wurin nema a Yanar-gizonmu ko a dangwala “Applicantion for Transcript”
5) Idan kana son neman ‘Re-forma certificate’ wanda ‘Re-forma’ da World Evangelical Alliance ke badawa, sai ka tabbata ka cika bangaren karshen na Manhajar.
-
- A karshe an shirya manhajar komai kamar littafin rubutu
- Kana bukatar kayi rigista na kos din aure a Yana-gizo. Ka dubi cikakken bayani a littafi rubutu.
Da zarar ka aika da shafin daya daya, zaka iya “neman satificaket na ‘Re-forma’ a yanar-gizo”
Labarai da dumi dumisu daga filin daga
Makarantar Live School
Schools
Dalibai
Kasashe
Manharjar Makarantar Live School
Makaranta Live School cikakkar makranta ce kuma ta kunshi duk abinda ake bukata domin koyon aikin Mishan da Almajirci, tana da kwasa kwasai 27 bidiyo na sa’a day a kowanne sashe wanda ke kokarin koyar da ‘yan kasa masu Bi a duniya baki daya a matsayin ‘yan kasa dake iya kafa Ikkilisiyai da zasu rayu kuma su kawo Bishara ga jama’arsu da makwabta.