Akwai abubuwa da yawa da za’a kula dasu wanda zaka bukaci daukar shawara kafin ka fara Makarantar Live School. Suna kamar haka:
Kafin ka kalli Bidiyo
1) Makarantar ana iya yinta na “cikakken lokaci” ko “rabin lokaci”.
-
- A Makrantar cikakken lokaci zaku bukaci ku shiga aji sau uku kowacce rana, zai dauke ka watanni 18 a gama.
- A makarantar rabin lokaci zaku bukaci yin watanni 18. Sai ku shirya yadda zaku raba manhajar bisa ga lokacin da zaku dauka.
- Hanya mai kyau ta gudanar da Makarantar shine, a hada iyali da abokai su hada akai don koyi. Ta wannan hanyar zaku taimaka wajen koyar da mutane dayawa don shelar Bishara ga batattu. Duk da haka, yana kyau idan zaka bi Manhajr don kashin kanka, musamman idan kana zaune a wurin dake da hadari ko kasar dake da matsala.
- Idan kuna kungiya, zamu so kusa wannen su yayi rigista a sashen yanar gizo don mu san irin cigaban da suke samu.
- Yafi kyau a ajiye lokaci domin Makarantar Live School domin kowa ya kasance da jaddawalin a hannusa.
- Wata hanyar kuma itace, kusa ‘yan kungiyarku su kalli sassan bidiyon a kadaice ko kungiyance na kashin kansu, su kuma tantauna tsakaninsu.
Yayin da kuke kallon
2) Sadda kuka zo tare, sai kuyi addu’a daga nan a nuna bidiyon, (yanada mahimmanci a fara duba yadda tsarin dukan bidiyon yake sashe sashe, daya bayan daya yadda aka shirya shi, saboda Makarantar an shiryata ta hanyar dake gina dadliban daga wannan mataki zuwa wannce).
-
- Lokacin da ake duba bidiyo sai ka rubuta abubuwan da sukayi maka fice.
- Da zarar an kamala sashen, ku dauki lokaci ku tantauna abinda kowa ya koya daga ciki. Ka kafafa kowa ya rubuta abinda ya tsallake a cikin rubuntunsa.
- Da zarar kun je gida, kuyi amfani da abinda kuka dauko a rubuce ku rubata shafi daya na abinda kuka koya, zaifi kyau a shirya shi kamar za’ayi wa’azi. (a shirya shi kwaya kwaya).
- Daga an a hau da wannan shafi gudan akan yanar gizo ta sashen mu. Zaku iya daukar hoto ku aika ba sai anyi amfai da ‘sikana’ ba.
- Ku boye wannan shafi daya a fayal doming aba.
- Ka ci gaba da bin wann hanya har a gama kos din.
Da zarar ka gama da sassan Makarantar Live School
3) Za’a baka satifiket na kamala Makarantar Live School muddin ka cika wadan nan sharudd guda uku.
-
- Ka bi ciki manhajar (awa 242).
- Ka aika da shafi dai dai din nan 242 a yana gizo.
- Ka nemi a baka satifiket dinka ta hannar Yanar-gizo kuma ka dangwala “Application for Certificate completion.”
4) Idan kana so ka kara karatu a South African Theological Seminary (SATS) ko Theolgical Institute of Argentina (FIFT), zaka iya ka nemi a baka shaidar takarda sassan da kayi ta wurin nema a Yanar-gizonmu ko a dangwala “Applicantion for Transcript”
5) Idan kana son neman ‘Re-forma certificate’ wanda ‘Re-forma’ da World Evangelical Alliance ke badawa, sai ka tabbata ka cika bangaren karshen na Manhajar.
-
- A karshe an shirya manhajar komai kamar littafin rubutu
- Kana bukatar kayi rigista na kos din aure a Yana-gizo. Ka dubi cikakken bayani a littafi rubutu.
Da zarar ka aika da shafin daya daya, zaka iya “neman satificaket na ‘Re-forma’ a yanar-gizo”